Tsohon shugaban mulkin kama kariya a Haiti Jean-Claude Duvalier ya koma kasarsa a karo na farko tun hambare gwamnatinsa a 1986.
Tsohon shugaban mulkin kama kariya a Haiti Jean-Claude Duvalier ya koma kasarsa a karo na farko tun hambare gwamnatinsa a 1986.
Kamin juyin mulkin,Duvalier,wanda aka fi sani da lakanin “Baby Doc”,ya yi mulkin Haiti tun 1971,bayan rasuwar mahaifinsa Francois “Papa Doc” Duvalier. Babu cikakken bayanin dalilin komawarsa kasar.
Ya koma kasar lokacinda Haiti take fuskanatar rikicin siyasa,da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da na wakilan majalisa,da kwariya-kwariyar sakamako da aka sake ya janyo zargin magudin zabe da zanga zanga cikin kasar.
Kamin komawarsa Haiti,Duvalier,ya yai zaman gudun hijira a Faransa.