Gidan Talabijin na kasar Tunisiya ya laburta cewa Ministocin Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar sun fice daga jam’iyyar da ta yi mulki ta hambararren shugaba Zine El Abidine Ben Ali. Wannan ya zo ne ‘yan kwanaki bayan murabus na ministoci hudu daga bangaren ‘yan adawa, wadanda suka ajiye aiki domin su nuna bacin ransu da cigaba da kakagidan da jam’iyyar ke yi a harkokin siyasar kasar. Ranar Litinin Firayim Minista Mohammed Ghannouci ya sanar da kafa gwamnatin Rikon Kwarya wadda ta gaji Ministocin Tsaro da na Cikin Gida da na Harkokin Waje daga tsohuwar gwamnati. Mr. Ghannouci da Shugaban kasar na wuccin gadi Fouad Mebazaa sun fice daga jam’iyyar ta RCD a wani yinkuri na nesanta kansu daga tsohon shugaban kasar. Ana sa ran sabuwar gwamnatin za ta fara taronta a hukumance a karo na farko gobe Alhamis. A halin da ake ciki kuma, sojojin kasar Tunisiya sun yi harbe-harben gargadi kan daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Tunis babban birnin kasar.
Ministocin gwamnatin rikon kwaryar kasar Tunisiya sun fice daga tsohuwar jam'iya mai mulki.