Yawan mutane da mummunar ambaliyan ruwa da laka suka kashe a Brazil ya kai akalla mutane 610, kuma akwai fargabar akwai wasu da dama da bala’in ya rutsa dasu a wasu yankuna masu nisa inda masu aikin ceto har yanzu basu sami damar zuwa ba.
Ci gaba da munin yanayi ya hana masu aikin ceto kaiwa ga mutane masu yawa da suka makale a sassan masu tuddai dake gabashin Rio de Janeiro.
A kasar Sri Lanka kuma jami’ai sukace sun gano Karin gawarwakin mutane jiya Asabar,wanda ya kawo adadin wadanda bala’in ya halaka zuwa 37. Akwai wasu da dama kuma da har yanzu baa san inda suke ba.
A Australia kuma,dubban ne suka fito jya Asabar domin bada gudumawarsu kyauta domin share kwatanni,da wasu shara da mummunar ambaliyar ruwa data aukawa kasar a birnin Brisbane jiya Asabar.