Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Brazil ta ayyana zaman makoki na kwana uku domin tunawa da a kalla mutane 610 da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa


Jerin akwatunan gawawaki a Brazil.
Jerin akwatunan gawawaki a Brazil.

Kasar Brazil ta ayyana zaman makoki na kwana uku domin tunawa da a kalla mutane 610 da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa.

Kasar Brazil ta ayyana zaman makoki na kwana uku domin tunawa da a kalla mutane dari shida da goma da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da dagwalon tabo. Ana fargaban cewa, akwai Karin mutane da dama da suka mutu a kauyukan da masu aikin ceton rayuka basu iya isa ba. An ayyana zaman makoki na kwana bakwai fara daga gobe Litinin, a jihar Rio de Janeiro yankin da ambaliyar tafi muni. Rashin kyaun yanayi da ake ci gaba da fama da shi, ya kawo cikas a yunkurin masu aikin ceto rayuka na isa wuraren da mutane suka kasa gaba ko baya a kauyukan dake tsaunuka. Har yanzu akwai gawawaki da dama da tabo da kuma baraguzai suka binne. Jami’ai suna fargaban cewa, ruwan sama da kuma kwararrar dagwalon tabo zasu kara haddasa asarar rayuka a cikin kwanaki masu zuwa. Wadanda suka tsallake rijiya da baya suna zargin hukumomi da gaza kai tallafin da ya kamata. An bayyana lamarin a matsayin bala’i mafi muni da kasar ta taba fuskanta.

XS
SM
MD
LG