Hada Hannu Don Nemawa ‘Yan Gudun Hijira Mazauni Na Din Din Din

Loogoo UNHCR

Kungiyar Tarayyar Kasashen Turai da Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira da wadanda suka rasa Matsuguni da Bakin Haure wato UNHCR tareda gudumawar Majalisar Dokokin Najeriya, za su tabbatar cewa an sama wa yan gudun Hijira da wadanda ta'addancin Boko Haram ya raba su da gidajen su wuraren zama na dindin cikin hanzari.

Bayanai dake fitowa daga sansanonin ‘yan gudun hijira musammam daga jihar Bauchi ta tsakiya, na nuni da cewa ‘yan gudun hijirar na fuskantar kalubalen tsadar rayuwa, da na rashin abinci da ruwan sha. Hakan yasa ‘dan majalisa mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Shehu Aliyu Musa, ya kawo kuduri a majalisar wakilai inda ya nemi gwamnati ta kawo dauki.

A dai dai lokacin da aka saurari kudurin ‘dan majalisar, shugabar hukumar kula da yan gudun hijira da wandanda suka rasa matsugunnan su, Hajiya Hadiza Sani Kan Giwa, tace akwai shiri na musammam da za a yiwa ‘yan gudun hijirar kafin a samar musu da gurin zama na din din din, idan an sami cikakken tsaro a yankin.

Ganin wannan yunkuri da gwamnatin kasa keyi ne yasa baban Jami'in Kugiyar Tarraiyar Turai Mr Michel Arrion ya kira taron manema labarai a Abuja, ya kuma jaddada irin taimakon da kungiyar zata bayar.

Your browser doesn’t support HTML5

Hada Hannu Don Nemawa ‘Yan Gudun Hijira Mazauni Na Din Din Din - 3'05"