Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tallafawa Kungiyoyi Don Taimakawa Sauran ‘Yan Gudun Hijira Dake Sansanoni


'Yan gudun Hijira
'Yan gudun Hijira

Yanzu haka kungiyoyin kare hakkin Dan Adam na nuna damuwarsu game da halin da yan gudun hijira da hare haren Boko Haram ya shafa tare da yin kira ga gwamnatocin Arewa da su hada hannu wajen tallafawa.

Wannan na zuwa ne yayin da yan gudun hijiran da aka kwato yankunansu ke neman da a maida su garuruwansu. Su dai wadannan ‘yan gudun hijirar da yanzu suka rage a sansanonin da aka tanadar, na yabawa da irin kulawar da sukace hukumomi na yi musu a yanzu. To amma sun bakaci a mayar da su gida tunda hankula sun fara kwantawa.

Hukumomin bada agaji sunce yanzu haka akwai shirye shiryen da akeyi na ganin an tallafa tare da sake tsugunnar da al’umomin dake komawa. Jami’in hukumar kula da agajin gaggawa ta NEMA mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, Alhaji Sa’adu Bello, ya bayyana irin matakan da ake ‘dauka.

Yanzu haka ma kwamitin sake farfado da yankunan da aka lalata dake karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro Janaral TY Dan Juma, da kuma hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dan Gote, sunce muddin ana son sake tsugunnar da mutanen da lamarin ya shafa, to tabbas za a kashe kudi kusan Naira Trillion biyu, wanda haka ne nunin akwai jan aiki gaban mai gona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG