Rahotanni sun ce matar mai shekaru 28 ta fara zazzabi ne tare da nuna alamun kamuwa da cutar bayan da ta dawo daga wata jana’iza a jihar Ebonyi.
Cutar ta Lassa wacce ake kamuwa da ita daga beraye ta yi kamari a wasu sassan Najeriya.
Tun a karshen shekarar da ta gabata ne cutar ta kunno kai inda mutane da dama suka kamu da ita yayin da wasu ma suka rasa rayukansu.
jami'an kiwon lafiyar kasar sun ce tsabta na daga cikin matakin farki da mutane za su dauka domin kare kansu daga cutar.
Sannan akwai bukatar a daina barin abinci a bude musamman inda beraye ke shawagi.
Saurari wannan rahoton wakilin Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan domin samun karin bayani kan bullar cutar a jihar Ogun: