Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto Ta Arewa: An Yi Watsi Da Karar Hassan


Court Nigeria
Court Nigeria

Takaddamar siyasa ta kaure a karamar hukumar Sokoto ta Arewa ta kai ga an garzaya kotun domin neman mafita game da wanda ya kamata jam’iyyar APC ta tsayar takarar a zaben kananan hukumomi.

Wata kotu a jihar Sokoto ta yi watsi da wata kara da Abdullahi Hassan na Jam’iyyar APC mai neman takarar shugabancin karamar hukuma.

Hassan ya ce shi ne ya lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gabatar ba wanda jam'iyya ta mikawa hukumar zaben jihar ba.

Karraki biyu ne kotun ta saurara a lokaci guda baya ga karar da Hassan ya shigar na dora wani a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

Sai kuma karar da ita kanta jam’iyyar ta APC ta shigar inda ta ke ikrarin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar ta Hassan.

Ga karin bayani game da wannan shari’a a rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG