Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya

Maihoras da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, ya ce ya cire ransa wajan zawarcin dan wasan gaba na Real Madrid dan kasar Wales, Gareth Bale, inda a jiya dan wasan yake bayyana sha'awarsa na ci gaba da zama a kungiyarsa ta Real Madrid, bayan an tashi a wasan da suka doke Manchester 2-1 a wasan UEFA, Super Cup.

Barcelona ta ce zatayi kokarin kammala cinikin dan wasan gaba na Liverpool Philippe Coutinho, nan da karshen mako, Barcelona ta saka fam miliyan £120, sai kungiyar ta Liverpool tace ba na sayarwa bane.

Har ila yau kungiyar Barcelona ta tura wakilanta zuwa kasar Jamus, domin kammala sayen dan wasan Borussia Dortmund, Ousmane Dembele, wanda takeso ya maye gurbin dan wasanta Neymar da ya Koma PSG.

Chelsea ta tura wa Arsenal tayin fam miliyan £25, kan sayen dan wasan tsakiyarta Alex Chamberlain.

PSG ta ce a shirye take wajan ganin ta sayo dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez, akan kudi fam miliyan £80.

An warware ciniki tsakanin Everton da Swansea City kan dan wasan tsakiya na Swansea mai suna Sigurdsson dan kasar Iceland.

Your browser doesn’t support HTML5

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya - 4'12"