Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NASA Ta Kara Aika 'Yan Sama Jannati Uku Don Zurfafa Bincike A Duniyar Wata


‘Yan sama jannati uku sun isa tashar kasa-da-kasa a duniyar wata, wanda ya bama hukumar binciken sararrin samaniya ta NASA, karin masana hudu a sararrin samaniya. A karon farko hukumar nada mutane hudu kenan da suke gudanar da bincike a duniyar wata.

Masannan sun isa duniyar watan da karfe 5:54 na yamma, an dai ware makudan kudade don gudanar da binciken, masannan sun kara nosawa cikin duniyar da tafiya fiye da nisannan kilomita 400, inda suke wuce tsararrakin su masana ‘yan kasar Rasha.

Masannan zasu haddu da sauran ‘yan sama jannatin na wasu kasashe goma sha biyar, don gudanar da aiki. Yanzu haka dai kasar Amurka, nada masana hudu a duniyar, wadanda suka hada da masu bincike a bangaren kiwon lafiyar dan'adam, da wadanda suke bincike akan albarkantun sararrin samaniya.

Ana sa ran dai isar karin masanan zai habbaka binciken, da ake gudanarwa a duniyar, da zummar kammala shi cikin kankannin lokaci. Masannan dai sun fito daga sauran kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, da fade aji wajen binciken kimiyya da fasaha, Japan, Canada, wasu kasashen turai, da Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG