Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya

Ranar laraba 31/8/2016 ita ce rana ta karshe da za'a rufe hada hadar saye da sayarwar ‘yan wasan kwallon kafa gaba daya na wannan kakar wasannin sai kuma zuwa wani lokaci a bude.

Za'a rufe da misalin karfe 12 na dare agogon Nigerian, inda Kungiyoyin kwallon kafa da dama ke ta kokarin saye da sayarwar kafin wa'adin ya cika.

A yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta saka zunzurutun kudi har fan miliyan £32, domin sayen tsohon dan wasanta David Luiz, daga PSG, wanda yabar kungiyar Chelsea, shekaru 2 da suka wuce akan kudi fan miliyan £50.

Barcelona, kuwa ta kammala sayen dan wasan gaba na Valencia, mai suna Paco Alcacer, na tsawon shekaru 5.

Yanzu haka mai tsaron gida na Man City Joe Hart, ya tafi Kungiyar Torino, ta kasar Itali a matsayin aro.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta amince da sayen dan wasan Borussia Dortmund, Aubameyang.

Dan wasan dai ya buga wa kungiyar Dortmund wasanni sau 49 a inda zurara kwallaye har 39 a raga.

Your browser doesn’t support HTML5

Hada Hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya