WASHINGTON, DC —
Dan wasan kasar Argentina Lionel Messi, ba zai sami damar fafatawa a wasan da kasar sa watau Argentina, zata buga da Uruguay, na neman shiga gasar cin kofin kwallo na duniya wanda za’a yi a shekara 2018.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona,ne ta fitar da sanawar bisa raunin da Lionel Messi ya samu a cinyar sa.
Messi, na cikin wadanda aka fidda sunayensu bayan rattaba hannu da yayi na komawa sake bugawa kasar sa wasan kwallon kafa bayan a can baya ya furta cewa ya rataye takalmansa na takawa kasar sa leda.