Hada Hadar Kasuwanci Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallo Ta Sauya Salo

Dan wasan PSG Adrien Rabiot, mai shekaru 23, da haihu zai iya barin Paris St-Germain idan zakarun na gasar Ligue 1 suka sayi takwaransa na Faransa N'Golo Kante, mai shekaru 27, daga Chelsea.

Kocin Chelsea, Maurizio Sarri, ya shirya domin tattaunawa da dan wasan Brazil Willian, mai shekara 29, yayin da Real Madrid da Manchester United da kuma Barcelona ke sha'awar sayen dan wasan.

Manchester United ta cimma wata yarjejeniyar sirri tsakaninta da kungiyar Barcelona, kan sayen dan wasan bayanta Yerry Mina, mai shekaru 23 dan kasar Columbia.

Newcastle, tana sha'awar sayen dan wasan baya na gefen hagu daga kungiyar PSG mai suna Stanley N'Soki, dan shekaru 19, wanda yake cikin tawagar ‘yan wasan kasar faransa ‘yan kasa da shekaru 20.

Manchester United, tana duba yuwar Sanya dan wasan gabanta Anthony Martial, dan shekaru 22 da haihuwa cikin sayen dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandowski dan shekaru 29.

Dan wasan tsakiyar Serbia Sergej Milinkovic-Savic zai ci gaba da zama a kungiyar Lazio a wannan kakar, an alakanta dan wasan, mai shekaru 23 da komawa Manchester United da Chelsea, a wannan lokacin bazarar.

AC Milan ta shirya domin sayen wani dan wasan da Chelsea ke nema dan wasan bayan Juventus, da Italiya, Mattia Caldara, mai shekaru 24 bisa wata yarjejeniyar musaya da za ta hada da dan wasan bayan Italiya, mai shekaru 31, Leonardo Bonucci, Sai dai kuma Chelsea ba ta yanke kauna ba kan sayen Higuain, kuma za su iya sayar da dan wasan gaban Faransa, mai shekaru 31, Olivier Giroud ga Marseille domin samun kudin yarjejeniyar.

Your browser doesn’t support HTML5

Hada Hadar Kasuwanci Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallo Ta Sauya Salo