Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaratan 'Yan Wasan Da Kungiyoyi Ke Zawarcinsu


Dan wasan baya na kungiyar Chelsea, dan kasar Brazil David Luiz, mai shekaru 31da haihuwa ya nuna sha'awarsa Ta cigaba da zama a kungiyar sakamakon zuwan Sabon Kocin Sarri, kungiyar Chelsea.

AC Milan tana shirin dauko tsohon Kocin Chelsea Antonio Conte domin ya maye mata gurbin kocinta Gattuso in haka ta kasance AC Milan zata rika biyan Conte kudi fam miliyan 5.5 duk shekara a matsayin albashi.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Niko Kovac yace dan wasan gabansa Robert Lewandowski, dan kasar Poland zai cigaba da zama a kungiyar, har zuwa wasu shekaru.

Ana alakanta dan wasan da komawa kungiyar Manchester united, da kuma Real Madrid, kungiyar Napoli tana sha'awar daukan dan wasan baya na Manchester united Matteo Darmian, dan shekaru 28, da haihuwa a matsayin aro bisa yarjejeniyan sayansa a karshen kakan wasa bana.

Real madrid tayi tayin fam miliyan 100 kan wasu ‘yan wasan Chelsea mai tsaron raga Courtois, mai shekaru 26, da haihuwa da kuma dan wasan tsakiya na Chelsea dan kasar Brazil, William wanda ake alakantashi da Manchester united ko Barcelona.

Har ila yau Kungiyar Chelsea tace zata koma zawarcin dan wasan baya na kungiyar Juventus, mai suna Mattia Caldara, dan shekaru 24 a duniya maimakon Gonzalo Higuain, mai shekaru 30 wanda ake alakantashi da komawa kungiyar Chelsea daga Juventus.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, ya bukaci 'yan wasansa irin su Jesse Lingard, dan wasan Ingila, da Romelu Lukaku na Belgium, da kuma dan wasan Faransa Paul Pogba da su yanke hutun da suke yi na dawo daga gasar cin kofin duniya da aka gudanar a bana domin hadewa da tawagar kungiyar a a shirye shiryenta na fara lig din bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG