Kungiyar kwallon kafa ta Manchester united tana bukatar tsohon Kocin Real Madrid Zinadine Zidane, da ya maye mata gurbin kocinta José Mourinho in har zai bar kungiyar.
Inter Milan ta nuna sha'warta ta dauko dan wasan tsakiya na Real Madrid Luka Modric, wanda yanzu haka yake hutun sa a kasar Italiya.
Chelsea, ta ce tana da karfin guiwa wajan samun nasara akan kungiyar Real Madrid kan sayen dan wasan gaba na Bayern Munich, dan kasar Poland Robert Lewandowski.
Har ila yau Chelsea, tana shiri wajan ganin ta inganta albashin dan wasan tsakiyar ta N'Golo Kante, dan shekaru 27, da haihuwa inda ta ce zata rika biyansa kudi fam dubu 290, duk sati a matsayin albashi.
Chelsea, ta ce yin hakan zai iya sa dan wasanta Eden hazard, ya cigaba da zama a kungiyar maimakon komawarsa Real Madrid. Sai dai har yanzu kungiyar PSG ta ce bata cire tsammani ba wajan sayen Kante daga kungiyar ta Chelsea.
Tottenham, tana zawarcin dan wasan gefe na kungiyar Crystal Palace, mai suna Wilfried Zaha, mai shekaru 25 a duniya akan kudi fam miliyan £45m.
Barcelona, tana sha'awar ganin ta sayo mai tsaron raga na Liverpool dan kasar Belgium, mai suna Simon dan shekaru 30 a duniya.
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce zai tura matashin dan wasan gabansa mai suna Ben Woodburn, dan shekaru 18 da haihuwa zuwa kungiyar Sheffield United, a matsayin aro domin dan wasan ya samu damar buga wasanni ta hanyar da zai sa ya kara gogewa a wasan.
Dan wasan gaba na kungiyar Juventus Gonzalo Higuain, ya amince ya koma kungiyar AC Milan, a matsayin rance da yarjejeniyar sayensa akan kudi fam miliyan 35 nan gaba.
Sabon Kicin Real Madrid ya tunkari dan kwallon gaba na Liverpool, Masar Mohamed Salah, dan neman yazo ya maye gurbin Cristiano Ronaldo bayan da Juventus ta sayeshi a bana.
Tsohon dan wasan gaba na Arsenal dan kasar faransa Thierry Henry, ya amince da ya karbi jagoranci mai horaswa na kungiyar kwallon kafa ta kasar Masar.
Facebook Forum