Dan wasan Najeriya Ahmed Musa da ke taka leda a kungiyar kafa ta Leicester City a Ingila zai koma kasar Saudiya da buga kwallo.
Kafofin yadan labaran cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa Musa zai koma kungiyar Al Nassr akan kudi fam miliyan 25 na Ingila.
Rahotanni sun ce Musa zai isa kasar ta Saudiyya a gobe Asabar domin karkare shirye-shiryen komawa kungiyar ta Al Nassr.
Idan har aka kammala cinikin dan wasan, Musa zai zamanto dan wasa mafi tsada cikin 'yan wasan Najeriya da ke buga kwallo a kasashen waje.
Kungiyar ta Al Nassr, na daya daga cikin manyan-manyan kungiyoyin kwallon kafa a Saudiyya.
Ta lashe kofuna 24 a gasa daban-daban da aka yi a kasar da sauran yankunanta.
Musa shi ne dan wasan da ya fara zirawa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha a wasanta da Iceland, inda ya ci duka kwallaye biyu a wasan da aka tashi 2-0.
Ya taba bugawa kungiyar CSKA Moscow kwallo a Rasha inda daga bisani ya koma Leiscester City, ko da yake, ya taba komawa CSKA Moscown a matsayin dan wasan aro daga kungiyar ta Leicester.
Facebook Forum