Ethiopia da Eritrea, sun sanya hanu kan wata yarjejeniya a wani taron koli da suka yi a kasar Saudiyya, matakin da ya kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, wadanda suka kwashe shekaru 25 suna yaki da juna.
WASHINGTON D.C. —
Ba a bayyana dalla-dalla ba sharuddan da suke kunshe cikin yarjejeniyar da kasashen suka rattabawa hanu da sarki Salman na saudiyya da babban sakataren MDD Antonio Gutierres suka shaida.
"Yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hanu a jeddaha a gaban khalifan wurare ibada masu tsarki, abune da zai shiga tarihi kuma gagarumin ci gaba ga mutane Ethiopia da Erirea, kuma zai taimaka wajen karfafa tsaro da daidaito a fadin yankin baki daya," in ji ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir, ta shafin Tweeter.
Eritrea, wacce ada lardi ne a kasar Ethiopia ko Habasha, ta balle ne a shekarar 1993. Rikicin kan iyaka ya haddasa yaki na tsawon shekaru 2 da ya halaka kimanin mutane dubu dari bakwai. Kuma zaman doya da manja ya biyo baya.