Jiya shugaba Muhammad Buhari ya sake mika sunayen mutane goma sha shida abun da ya kawo adadin sunayen da shugaban ya turawa shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki talatin da bakwai.
Sai majalisa ta tantance su 37 din kafin shugaban kasa Muhammad Buhari ya rantsar dasu ya kuma basu wuraren da zasu yi aiki
.Malam Sale Haliru da Farfasa Al-Mustapha Usuju da Garba Shehu sun yi tsokaci akan sunayen da batun tantancesu.
Bisa ga matsayin shugaban kasa Sale Haliru yace idan an samu wani daga cikin mutanen da wani abu da bai dace ba shugaban zai cire sunansa. Saidai abun da ake fama dashi yanzu shi ne koke-koken mutane akan wadanda basa so. Akwai kuma korafi akan jihohin da wasu suka fito.
Akan jinkirin da shugaba Buhari ya yi kafin ya mika sunayen wadanda zai nada ministoci Garba Shehu yace gyara da shugaban yake yi ya jawo hakan. Yace shugaban ya samu gwamnati a gurbace. Ya samu gwamnati inda dukiyar jama'a dibanta ake yi. Dole ne ya soma yin gyara kafin mika sunayen ministocin.
Shi ma Farfasa Al-Mustapha Usuju yace idan majalisa ta karbi koke-koke tana bincike a kai. Idan koken na gaban kotu majalisa ba zata yi komi ba sai kotu ta yanke hukunci. Sanatoci da suka fito daga jihohin wadanda aka mika sunayensu zasu yi magana. Sai hujja mai karfi ce zata sa majalisa ta ki amincewa da nadin mutum.
Ga karin biyani.
Your browser doesn’t support HTML5