Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani Kan Matakan Tantance Ministoci


Senator Bukola Saraki looks on after being elected as the senate president of the 8th Nigeria Assembly in Abuja, Nigeria June 9, 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX1FRVG
Senator Bukola Saraki looks on after being elected as the senate president of the 8th Nigeria Assembly in Abuja, Nigeria June 9, 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX1FRVG

Tun bayan da aka fitar da sunayen da shugaban Najeriya Muhammadu ya mikawa Majalisar Dattawa, masana da masu fashin baki suka fara tambaya ko matakan da za majalisar za ta bi wajen gudanar da wannan aiki zai karkata ne akan siyasa ko cancanta.

A makon da ya gabata shugaba Muhammadu Buhari, ya mika sunayen mutane 21 a gaban Majalisar, a matsayin wadanda zai baiwa mukaman ministoci, kuma tun bayan hakan ne ake ta cecekuce kan wadannan sunaye.

“Wasu ka’idoji sababbi da ake neman kawo wa, ka’idoji ne wadanda idan kika duba za ki ga suna da nasaba da siyasa, kamar misali cewa sanatoci guda biyu daga jahar ka sai sun amince da kai kafin a iya wanke ka.” In ji Barrister Main Nasar Ibrahim Faskari, masanin kundin tsarin mulki da zamantakewar dan adam.

Ya kara da cewa, “maganar sanatoci guda biyu su wanke ka ba ta taso ba, majalisar dattawa aka ce ta duba gaba daya ta wanke shi, ma’ana idan mafi yawan ‘yan majalisar nan suka wanke ka shi Kenan.”

Barrister Faskari ya kuma kara da cewa, mafi yawan ministocin da aka ba da sunayensu ‘yan jam’iyyar APC ne, “yaya za a yi da kasashen Igbo wadanda ba su da dan majalisa dan APC ko kwaya daya, duk ‘yan jam’iyyar PDP ne.”

A cewarsa, banbancin ra’ayin siyasa zai iya kawo tarnaki domin wadanda ba ‘yan APC ba za su ce bari su hana wani dan jam’iyyar ya wuce.

KORAFE-KORAFE KAN SUNAYEN MINISTOCI

Wani abu yanzu da ya fi daukan hankali mutane da dama shi ne koke-koken da aka gabatarwa majalisar daga juhohin da suka fito, wanda shi wasu ke ganin zai yi tasiri wajen aikin tantance mutanen.

Daga cikin korafe-korafen da suka fi daukan hankula, akwai wandanda sukasamo asali daga jahar Rivers kan tsohon gwamnan jahar Rotimi Amaechi da kuma Hajiya Amina Muhammed, wadda Kaduna da Gombe ke kalubalanta.

Domin jin yadda jam’iyyun PDP da na APC ke kallon wannan takaddama da kuma matakan tantance sunayen mutanen, saurari karashen wannan rahoto da Medina Dauda ta aiko mana daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG