Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nadin da Gwamnan Taraba Ya Yi Ya Tayarda Kura


Sanata A'ishah Jummai Alhassan, yar takarar gwamna ta jam'iyyar APC
Sanata A'ishah Jummai Alhassan, yar takarar gwamna ta jam'iyyar APC

Gwamnan jihar Taraba ya nada mutane 112 a matsayin masu bashi shawara kan ya nada kwamishanoni 20

Sabbin nade naden sun raba kawunan 'ya'yan jam'iyyar PDP dake jihar.

Wasu 'yan jam'iyyar suna zargin ana nuna masu wariya da son kai. Wani Alhaji Kabiru Zakari na jam'iyyar PDP a jihar yana zargin cewa duk wadanda aka nada babu Hausa ko Fulani daya cikinsu.

Wasu da suka ce suna cikin jam'iyyar tun 1999 har zuwa yanzu sun ce an yi watsi dasu.

Ba 'yan PDP ba ne nade-naden ya bata wa rai hatta na jam'iyyar adawa ta APC sun bayyana rashin jin dadinsu. Alhaji Hassan Mika shugaban APC na jihar yace abun kunya ne irin abun dake faruwa a jihar yanzu.

'Yan APC suna mamakin yadda gwamnan zai biya wadanda ya nada ganin cewa ko albashi bai iya biya ba. Kudin fansho baya biya. Ma'aikatan kananan hukumomi suna nan babu albashi. Haka ma sarakuna.

Gwamnan jihar ya mayarda martani ta bakin hadiminsa ta fuskar siyasa Alhaji Abubakar Bawa. Ya musanta zarge zargen. Yace jihar bata da masana'antu saboda haka wajibi ne a kawo mutane cikin gwamnati saboda su ci alfarmar gwamnatin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG