Matsalar na yi masu barazanar rashin iya biyan albashi a jihohi da dama. Wasu jihohin da suka biya albashin suna ganin cigaba da biya ba zai dore ba matukar basu samu wasu makudan kudade ba da zasu dinga biyan albashi da cika alkawuran da suka yi lokacin kemfen.
Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara shi ne shugaban kungiyar gwamnonin wanda yana ganin matsalar ruwan dare ce gama gari. Yace akwai jihohin da ba'a biya albashi ba na watanni shida ko fiye da haka. Yace ba jihohi kadai ba ne suke fama da karancin kudi har da gwamnatin tarayya.
Gwamna Yari yace sun tattauna kuma zasu gana da shugaban kasa domin samun masalaha akan yadda za'a fita daga kangin da suka shiga saboda kasa ta cigaba.
Yace wannan gwamnatin Allah ya kawota kuma suna da tabbacin cewa duk da ta shigo cikin wani mawuyacin hali da suka shafi rashin kudi da yadda ake gudanar da baitulmalin gwamnati, za'a samo bakin zaren.
Gwamna Muhammad Abubakar na jihar Bauchi ya aza laifin akan gwamnatocin da suka shude musamman a irin jihohinsu da aka samu sauyin ragamar jam'iyya. Yace duk gwamnati dake da adalci idan ta karbi kudi ma'aikata ake fara biya. To amma a jihar Bauchi da an samu kudi sai a fara biyan manyan 'yan siyasa dake rike da mukamai har da ma kudin sallama da kuma masu hannu da shuni.
Masana tattalin arziki na ganin bunkasa hanyoyin samun kudin shiga kamar tono ma'adanai da sauransu ne kadai zai rage dogaro ga kudin man fetur.
Barrister Rigachukun Ibrahim da ya taba rike mukamin kasuwancin majalisar wakilai na ganin sai Najeriya ta kara dagewa wurin kare muradun 'yan kasuwanta dake zai jawo zuba jari a kasar.
Barrister Ibrahim ya nuna rashin gamsuwa da yadda shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya wofintar da batun farwa baki a kasarsa a lokacin da aka gudanar da taron kungiyar kasashen Afirka a can kasar.
Gwamnatin Jonathan da ta shude ta fitar da Najeriya a matsayin kasar da tafi karfin tattalin arziki a Afirka to saidai labarin sai an ciwo bashi a biya albashi ya jefa tababa ga batun.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5