Jami'an tsohuwar gwamnatin jihar Niger na ci gaba da mayar da martini kan matakin da gwamnati mai ci yanzu ta dauka na binciko wasu kudade da aka zargi gwamnatin da ta shude da cewa ta karba bashi.
A wani taron manema labarai da ya kira, Alhaji Idris Ndako, jami'i a tsohuwar gwamnatin ya ce batun kudade naira miliya dubu uku da aka ce sun ciwo bashi kuma sun raba wa kawunan su a dai-dai lokacin da suke daf da barin mulki kage ne kawai.
‘’Irin wannan bashin da aka ce mun ciwo kowa a kasar nan ya san cewa tun cikin watan Janairu na wannan shekaran gwamnatin tarayyar da ta wuce na shugaba Jonathan sun riga sun rubuta wa dukkan bankuna cewa kar a baiwa kowace jiha rance to ina ne mu muka samu namu?’’
Yanzu kana nufin baku karbo bashin wadannan biliyan ukku da suke Magana ba?
‘’A ina ni ban san da wannan bashin da suke Magana ba wa zai bamu, idan ance mun karbi bashi to wurin wa? Yaushe? Wannan mu dai bamu san dashi ba ni dai a matsayi na na sakataren gwamnati kuma duk wani tafiyan da talba keyi duk wasu abuwa da akeyi ana tattauna su a majilisar gudanarwan jihar, kuma nine sakataren wannan majilisar , banji kuma banga inda aka ciwo bashi ba.’’
Kun dai ga alaman wadannan mutanen shine su bincike ku baku da wani fargaba kuna da bayanin da zaku kare kanku?
‘’ALLAH shine ke kare mutum jawabi ba nayi maka jawabi ba yanzu akan abin da na sani kuma tsakani na da ALLAH, Mu mutanen Niger ne ni mutumin Niger kuma duk abinda zai cuci jihar Niger wallahi sai inda karfi na ya kare’’.
Sai ko jiya ranar alhamis ma Gwamna Abubakar Sani Bello ya sjhaidawa manema labarai cewa ba zasu bata lokaci ba wajen gudanar da bincike ba, sai kuma ko bayan tiya akwai wata caca inji yan Magana.
‘’Bance kuma idan anyi banna za a barshi a hakanan bay au satin mu biyu Kenan a ofis kuma muna mayar da hankali ne wajen gyara tukun na, dominidan ka bata lokacin wajen bincuike nan bincike can sai ka bata lokaci ba ayi wani abin kirki ba, sai ko shakka babu idan muka ga anyi rashin adalci ko an zalunci mutum zamu kirawo mutum yazo yayi bayani yadda yayi da dukiyar jamaa’’
Sai dai kawo yanzu ba wani bayani da aka ji daga bakin tsohon gwamna Babangida Aliyu game da wannan badakala.Sai dai daga bakin mukarabban sa.