Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Koka Da Tabarbarewar Tsaro A Yankunansu

Gwamnan Katsina Dikko Radda da Janar Lagbaja

Gwamnan Katsina Dikko Radda da Janar Lagbaja

Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya na ta rige- rigen zuwa hedkwatar rundunar sojojin Najeriya don neman karin dauki bisa tsanantar aika-aikar 'yan bindiga dadi a yankunansu.

Ziyara ta baya-bayan ita ce wacce Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya kai.

Radda wanda ya gana da Babban Hafsan Hafsoshin mayakan Najeriyar, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya ce a halin yanzu suna cikin ukubar yan bindiga dadi, barayin shanu da sauran gungun masu aikata manyan laifuka.

A cewar shi, kananan hukumomi takwas da suka hada da Sabuwa, Jibia, Batsari, Safana, Dandume, Faskari, Danmusa har izuwa Kankara na kan iyaka da dajin Rugu da hakan ya sa yan bindigar ke samun sukunun kaddamar masu da hare-hare.

Babban Hafsan Hafsoshin ya ce za a sake daukar karin matakan tunkarar 'yan bindigar don samawa jama’a sauki.

Wani Mazaunin yankin Danmusa, Alhaji Bashar Danmusa da yake Muryar Amurka bayanin girman matsalar, ya ce kusan kowanne lokaci suna cikin ukubar 'yan bindigar da ke sace mutane ko ma kashe su dungurungum a ciki da wajen garin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnonin jihohin arewa ta yamma da ta tsakiya ke wanke kafa su ziyarci hedkwatar sojojin ba da nufin neman karin dauki bisa tabargazar 'yan bindigar.

Ko a baya-bayan nan, sai da gwamnonin jihohin Neja, Kaduna da Nasarawa suka kawo irin wannan ziyara.

Ziyarar da wani mai fashin baki a harkar tsaro ke cewa, ba ta da wani muhimmamci.

Basharu Altine Guyawa Isa ya ce kamata ya yi a ce sojoji sun san daman wannan aikinsu ne ba sai wani gwamna ya koka masu ba.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Koka Da Tabarbarewar Tsaro A Yankunansu