Gwamnatocin Tarayya Da Na Jihohin Najeriya Na Tunanin Kirkirar ‘Yan Sandan Jihohi

'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

Gwamnatocin tarayya da na jihohin Najeriya 36 na nazari akan bukatar kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi.

Hakan ta biyo bayan wani taron gaggawa daya gudana yau, Alhamis 15 ga watan Fabrairu, tsakanin Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da gwamnonin kasar a fadarsa ta Aso Rock.

Taron na zuwa ne sakamakon karuwar matsalolin hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa da rashin tsaro a fadin Najeriya a ‘yan kwanakin baya-bayan nan.

A jawabinsa ga manema labaran fadar gwamnatin jim kadan bayan kammala taron, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan al’ummar Najeriya, Muhammad Idris, ya bayyana cewar har yanzu ba’a kai ga cimma matsaya akan batun ba, amma komai zai fito fili idan aka samu karin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsakin.

A saurari rahoton Umar Farouk:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatocin Tarayya Da Na Jihohin Najeriya Na Tunanin Kirkirar ‘Yan Sandan Jihohi