ABUJA, NIGERIA - Gwamnatin kasar ta bakin Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin tarayyar kasar, Abuja inda ta fayyace cewa zata fara raba wa ‘yan kasar hatsi tan dubu 42 kyauta kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shirin.
Ko yaya gwamnatin kasar zata tantance mabukata da ya kamata su ci gajiyar wannan tallafi, ganin yadda a baya an sha ganin yadda wasu marasa kishin al’umma ke karkatar da ababen da ya kamata talakawa su ci moriya, Sanata Abubakar Kyari ya ce gwamnati za ta hada kai ne da kungiyoyin manoma da na sarakunan gargajiya don tabbatar da cewa tallafin ya kai ga wadanda ya kamata su ci gajiyar shi.
A game da batun yadda gwamnonin jihohi za su iya ba da tasu gudunmawa wajen rage matsalar yunwa baya ga kokarin gwamnatin tarayya, Sanata Kyari ya ce ganin yanayin da ake ciki duk sun fara tashi tsaye a samo bakin zare a kan yanayin.
Sai dai duk da wannan matakin da gwamnati ta dauka wajen rage radadin matsalar tsadar abinci da yunwa da ake fama da su a cikin Najeriya, tsohon kwamishinan yadda labarai na jihar Adamawa, Mallam Ahmad Sajoh, ya ce matsalar ta wuce tunanin gwamnati, yana mai cewa akwai marasa kishin kasa dake yiwa dukkan shirye-shiryen gwamnati zagon kasa kuma ya kamata gwamnati ta yi la’akari da wannan.
Alkaluman kididdiga dai sun yi nuni da cewa, farashin kayayyakin abinci na ci gaba da hauhawa a Najeriya cikin 'yan shekarun da suka gabata, sai dai tashin farashi na watannin baya-bayan nan musamman daga watan Disambar shekarar 2023 ya zuwa yanzu ya kai inta’a, kuma ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da suka da ce cikin gaggawa kar lamarin ya rikide zuwa babban rikici.
Rahotannin su yi nuni da cewa yan Najeriya miliyan 26 da dubu 500 na fama da rashin wadataccen abinci, inda ‘yan kasar ke kashe kaso 59 cikin 100 na abin da suke samu wajen abinci, sannan kuma akwai wasu ‘yan kasar miliyan 104 dake cikin tsananin talauci idan aka duba fuskar samun kudadden shiga.
Masana tattalin arziki da tsaro dai cun se alkalumman nan abun tsoro ne kuma babu wani abu da zai iya kasancewa da hadarin gaske fiye da tashin farashin kayan abinci wanda zai iya yin mumunar tasirin ta fuskar rashin tsaro da bunkasar tattalin arziki, ko ci gaban ɗan adam da tsaron ƙasa.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna