Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Buredi A Najeriya Na Shirin Tsunduma Yajin Aiki Saboda Tsadar Kayan Hada Buredi


Masu sayar da Buredi
Masu sayar da Buredi

Masu kamfanonin buredi a Najeriya sun ce suna daf da rufe kamfanoninsu saboda matsalar tashin gwauron zabi da kayan sarrafa buredin ke yi a halin yanzu.

Buredi dai na daya daga cikin abinci mafi sauki da al’ummar Najeriya ke amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum.

A wani taron manema labarai a birnin Lokaja fadar gwamnatin jihar Kogi, Shugaban kungiyar masu buga buredin a jihar Kogin, Cif Adeniyi Bamidele Gabriel, yace shugaban kungiyar masu kamfanonin buredi a Najeriya, Alhaji Munsir Umar, da kuma babban sakataren kungiyar sun amince da su tsunduma yajin aiki daga ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu idan har gwamnati ba ta yi kokarin shawo kan matsalolin tsadar kayan da suke amfani da su ba.

Masu buredi
Masu buredi

Haka zalika masu buga buredin sun koka akan tsawwala masu haraji daga gwamnatin Najeriya.

Shugaban kamfanin Shukura Bread a Najeriya, Alhaji Lawali Shukura, wanda shine mataimakin shugaban kwamitin amintattu na kungiyar a yankin Arewacin Najeriya, yace akwai bukatar hukumomin Najeriya su yi wani abu cikin gaggawa akan lamarin buredin da ke da matukar tasiri a rayuwar talakawa.

Wannan mataki na masu buredin dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kan matsalar tsadar rayuwa al'marin da gwamnatin Najeriya tace tana kokarin shawo kan shi.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG