Hakan na zuwa ne a yayin wani aikin share fage a kan tudun mun tsira inda aka gano wani keɓaɓɓen gini wanda ya zama masana'antar kera makamai da ke kan wani babban fili a ƙauyen Pakachi, cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.
A yayin aikin, an gano muggan makamai da na’urori masu alaka da su, tare da kuma kama wani wanda ake zargi.
An kama Mr. Tapshak Plangji, wani matashi mai shekaru 25 da haihuwa, wanda ake zargin yana da hannu wajen aikata haramtattun ayyuka a masana'antar.
Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Captain Oya James, a wata sanarwa ya ce wanda ake zargin shine ya mallaki masana'antar kera makaman wani Mr. Nuhu Meshack, wanda a halin yanzu yana nan a hannu ana kuma kokarin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Sanarwar tace kayayyakin da aka kwato daga wurin sun hada da bindigogi kirar AK 47 guda 5, mujallu kirar AK 47 guda 4, harsashi 11 na 7.62mm, albarusai 5mm da 9mm, bindigogi 21, bindigogin revolver 4, bindigogi 11 mai mujallu 5, gungun bindigogi mai jigida 17 na 0.44 incin ammonium, silinda carbide tare da Na'urorin haɗi.
Zarto guda 3, Filing Machines 12, guduma guda 4, injin tono 6, na'urar samar da wutar lantarki guda 2, G-Clamps 2 da Injin na feshi guda 1.
Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin Mr. Plangji, tare da bindigogin da aka kwato da sauran kayayyaki, a halin yanzu suna hannun rundunar domin ci gaba da bincike.
Rundunar sojin tace wannan nasarar da ta samu ya nuna jajircewar sojojin tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci a tsakanin al’umma.
Har ila yau, ta ce nasarar ta nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’ummar yankin wajen kare al’umma daga barazanar da ke tattare da kera makamai da safarar miyagun kwayoyi.
Dandalin Mu Tattauna