Gwamnatin Tarraya Da Jihohi Sun Raba Naira Biliyan 676 Daga Asusun FAAC A Watan Nuwamba

Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

Rahotanni sun yi nuni da cewa bangarorin gwamnatin Najeriya uku sun raba naira biliyan 675 da miliyan 946 daga asusun rabon arzikin tarayyar kasar wato FAAC a watan Nuwamba.

Mukaddashin daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Olajide Oshundun ne ya bayyana haka a ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 261 da miliyan 441 na kudaden, a yayin da jihohi suka sami naira biliyan 210 da miliyan 46, kananan hukumomi kuma suka sami naira biliyan 155 da miliyan 456.

Haka kuma jihohin da ake hako mai a cikinsu suka sami karin naira biliyan 49 da miliyan 3 daga kashi 13 na asusun hako man fetur.

Jumlar kudaden shiga na VAT da aka tara a watan Nuwamba ya kai naira biliyan 196 da miliyan 175 sabanin naira biliyan 166 da miliyan 284 da aka samu a watan Oktoba, wanda ya nuna karin naira biliyan 29 da miliyan 891.

Daga kudaden shiga na VAT, gwamnatin tarayya ta sami naira biliyan 27 da miliyan 402, yayin da jihohi suka sami naira biliyan 91 da miliyan 339, sai kuma kananan hukumomi da suka sami naira biliyan 63 da miliyan 937.

Hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya wato FIRS, hukumar kula da shige da fice ta Najeriya wato kwastam da hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya suka sami naira biliyan 7 da miliyan 847 a matsayin kudin gudanar da aikin tattara kudaden shiga yayin da aikin hukumar raya yankin Arewa maso gabas wato NEDC ya samu Naira biliyan 5 da miliyan 650.

Daraktan ma’aikatar kudi wato Oshundun ya kuma kara da cewa, kudaden shigar da doka ta kayyade na naira biliyan 643 da miliyan 481 da aka raba a watan Nuwamba ya haura naira biliyan 407 da miliyan 864 da aka samu a watan Oktoba da naira biliyan 235 da miliyan 617, inda gwamnatin tarayya ta sami Naira biliyan 231 da miliyan 863.