Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Ciwo Bashin Naira Triliyan 32.2 a Shekarar 2020


Mahawara ta kaure akan yadda Najeriya ta ciwo bashin da ya kai Naira Triliyan 32.2 ya zuwa karshen shekarar 2020, sai dai shugaban Majalisar dattawan kasar Ahmed Lawan ya ce kundin tsarin mulki ya ba majalisa dama ta sa ido akan yadda za a sarrafa kudaden har sai ta gamsu.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin kula da basussuka na kasa da ake kira DMO, ta ce bayanai akan yadda aka rarraba kudaden sun nuna cewa bashin cikin gida da Najeriya ta ci ya kai Naira triliyan 20 ko kashi 68.18 cikin 100 na jimlar basussukan, sannan bashin kasashen waje kuma ya kai kashi 37.82 cikin 100.

Ko da yake, sanarwar ta ce Ministar kudi da tsare tsare Zainab Shamsuna Ahmed, ta yi hasashen cewa bashin da ake bin kasar na iya karuwa kafin karshen wannan shekara ta 2021 saboda wasu ayyuka da aka amince a gudanar da su a cikin kasafin kudin wannan shekarar.

Kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shu'aibu Idris Mikati, ya nuna damuwa kan yadda kasar ke cin bashi duk da cewa gwamnatin tarayya na shirin daukar nauyin biyan basussukan daga cikin kasafin kudi na shekarar 2021 amma kuma za a sake karbo sabon rancen Naira triliyan 4.28 wanda ya kai kashi 1 cikin 3 na kasafin kudin da shugaban kasa Mohammadu Buhari ya riga ya sawa hannu,

To sai dai Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya yi tsokaci akan yawan bashin da kasar ta riga ta ci, inda ya bada tabbacin cewa majalisa a shirye ta ke ta goyi bayan karbo duk wani bashi da ta tabbatar za a sarrafa shi ne wajen inganta rayuwar jama'ar kasa, amma idan majalisa ta ga akwai akasi wajen aiwatar da kudin, to za ta yi amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen tsawatarwa.

Shi kuwa masanin tatalin arziki kuma Malami a Jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Muntaqa Usman, ya ce sun dade suna bada shawarwari akan hanyoyin da za a bi a samar wa kasa kudade ba ta hanyar cin bashi kawai ba, domin shi ya na ganin wadannan kudade da ake karbowa na 'yan jari hujja ne kawai.

Farfesa Muntaqa ya ce wasu 'yan kalilan ne ke azurta kansu ta hanyar karbo bashin da kuma ta yadda za a biya shi, kuma haka ya na iya sa kasa a wani hali na kaka-na-kayi, saboda haka idan kasa ta na so ta ci gaba sai shugabanni sun sauya dabi'unsu.

A yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido su ga irin ayyukan more rayuwa da gwamnati ta ce za ta yi da kudaden da ta karbo bashi a cikin gida da waje.

Saurara karin bayani a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG