Hukumomin Najeriya sun kafa kwamitin bincike wadda zata binciko da nazartar abinda ya janyo hargitisn siyasa.
hukumomin Najeriya sun kafa kwamitin bincike wadda zata binciko da nzarin abinda ya janyo hargitsin dake da nasaba da siyasa a babban zaben da aka gudanar a Najeriyan a watan da ya gabata.
Shugaba Goodluck Jonathan, Laraba yake bayanin cewa hukumar binciken mai wakilai 22 zasu gano adadin wadanda suka rasa rayukansu a lokacin hargitisn,su kuma gano hanyar da za'a hana irin haka sake afkuwa a Najeriya.Kazalika,hukumar zata kokarta binciko irin hasarar kadarorin da rikicin ya janyo.
Wata kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Najeriya tayi kiyasin cewa akalla mutane dari biyar ne suka halaka a dalilin hargitsin siyasar.