Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 17 da Talata 18 ga watan Yunin da muke ciki su zama ranakun hutun bukukuwan babbar Sallah.
A sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya taya al'ummar Musulmi dake ciki da wajen kasar murnar zagayowar wannan lokaci.
Ministan, a sanarwar, ya jaddada cewar gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta kudiri aniyar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar 'yan najeriya."
"Ya kuma kara yiwa al'ummar Musulmi da 'yan Najeriya nasihar cigaba da nuna goyon baya da hadin kai ga shugaban kasa a kokarinsa na fadadawa da bunkasa da kuma farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin hanzari."
"A yayin da yake yiwa al'ummar Musulmi fatan yin bukukuwan babbar sallah lafiya, ministan ya shawarci 'yan Najeriya su kudiri aniyar gadarwa 'ya'yansu kasa mai yawar arziki.
Tunda fari, rahoto ya gabata cewar shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja, fadar gwamnatin Najeriya, zuwa Legas a yau Juma'a domin bikin babbar Sallah.