SOKOTO, NIGERIA - Limamin dai ba wannan nan ne karo na farko ba da yake bijirewa umurnin Shugaban Majalisar koli kan lamurran addinin Musulunci a Najeriya, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar musamman kan batun da ya shafi ganin watan azumi Ramadan ko na Sallah.
A wannan shekara ma, Sheikh Lukuwa ya jagoranci magoya bayan sa wajen gudanar da Sallar ta Idi a Masallacin sa da ke shiyar Mabera da sanyin safiyar yau Talata.
Limamin ya kafa hujjar yin sallah da kuma ajiye azumi bisa ga samun rahotannin ganin wata a wasu wurare da ya hakikance da su a Jamhuriyar Nijar, duk da yake ya ce a Najeriya ma an samu wasu rahotanni na ganin watan Shawwal sai dai ba a tantance su ba.
Wannan Sallar dai ta sabawa umurnin Majalisar Koli kan lamurran Musulunci a Najeriya, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi wadda ta ayyana ranar Laraba 10 ga Aprilu a zaman ainihin ranar Sallar Idi, saboda ba a ga watan Shawwal ba ranar Litinin ta 29 ga Ramadan, saboda haka watan Ramadan zai cika kwana talatin ke nan.
Yanzu haka kusan dukkan Musulmi a Najeriya na dauke da azumi cikamakon na talatin kafin gobe Laraba su yi Sallar Idi.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna