Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamar Sallah: NSCDC Ta Tura Ma’aikatanta 40,000 Zuwa Sassan Najeriya


NSCDC
NSCDC

A wani yunkuri domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan Sallah Azumi cikin lumana, hukumar tsaro ta Civil Defence wato NSCD ta dauki kwararan matakai domin tabbatar da tsaro a yayin da ake fuskantar matsalar tsaro a kusan duk fadin Najeriya.

Hukumar NSCDC ta sanar da tura jami’ai dubu 40,000 a fadin kasar don tabbatar da tsaron al’umma a lokacin bukukuwan sallar bana.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar, CSC Babawale Afolabi ya ce matakin tura irin wannan adadi mai yawa na ma’aikata ya samo asali ne domin ganin an daukimatakan da suka dace wajen tunkarar kalubalen tsaro da ka iya tasowa.

Babban Kwamandan NSCDC, Ahmed Audi, ya umurci kwamandojin jihohi da su sanya ma’aikatan hukumar a muhimman wurare na jihohinsu.

NSCDC
NSCDC

A cikin sanarwa ya shaida cewa Hukumar NSCDC tana bin tsarin da ya dace, tare da hada dabaru don dakile ayyukan aikata laifuka a lokacin bukukuwan Sallah harma da ba lokacin bukukuwan Sallah ba a jihohi daban-daban. Wannan tsari da ya kunshi bangarori daban-daban na nuna jajircewar rundunar na kare rayuka, dukiyoyi, da muhimman kadarorin kasa.

A cikin wani sako da Dokta Ahmed Abubakar Audi, Kwamandan Rundunar NSCDC ya fitar, an bayar da tabbacin game da gudanar da bukukuwan lami lafiya. Dokta Audi ya jaddada shirin rundunar na tura jami’ai da mazaje zuwa wurare masu muhimmanci kamar wuraren taruwar jama’a, wuraren sallar idi, manyan kantuna, kasuwanni, wuraren shakatawa, wuraren aje motoci, da sauran wuraren a fadin kasar.

NSCDC
NSCDC

An dorawa kwamandojin Jihohi alhakin tabbatar da aiwatar da tsare-tsaren tura jami’an Hukumar ba tare da wata matsala ba, tare da karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

A ci gaba da shirye-shiryen Sallar Eid-El-Fitr, Dr. Ahmed Abubakar Audi ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi tunani a kan koyarwar watan Ramadan, inda ya jaddada muhimmancin nuna tausayi, hadin kai, da mutunta juna. Ya kuma jaddada muhimmancin tunawa da mafiya rauni a cikin al’umma da kuma mika fatan alheri ga kowa.

Yayin da al’ummar Najeriya ke shirin gudanar da bukukuwan Sallar Idi a ranar Laraban nan, hukumar NSCDC na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, tare da samar da yanayi mai kyau don gudanar da bukukuwan murna Sallah.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG