Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Saki Fursunoni 222 Gabanin Sallah


Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta yi afuwan da sakin fursunoni 222 da ba za su iya biyan tarar da kotuna daban-daban ta yanke musu ba gabanin bikin Sallah.

WASHINGTON, D. C. - Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce manufar ita ce rage nauyin fursunoni a fadin gidajen gyaran hali na jihar a cikin wannan watan na Ramadan da kuma bukukuwan Sallah mai zuwa.

Babban Lauyan jihar kuma kwamishiniyar shari’a Fadila Muhammad Dikko ce ta bayyana hakan a wata sanarwa.

Ta ce mutane 222 da suka ci gajiyar tallafin, an zabo su ne bayan an tantance su sosai, biyo bayan shawarwarin da gwamnatin jihar ta ba su na ta shiga tsakani.

"Ana sa ran aikin alherin da Gwamna ya yi zai rage cunkoso a wadannan wuraren tare da baiwa fursunonin da aka sako damar cin moriyar bikin Sallah tare da 'yan uwansu," in ji Fadila.

Da yake yabawa Gwamna Radda kan wannan shiri, babban mai shigar da kara na Katsina ya bayyana cewa, an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga cikin fursunonin da ake tsare da su bisa kananan laifukan kasuwanci da kuma wadanda laifukansu ba su kai minzamin manyan lafuka ba.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG