Gwamnatin Taraba ta Debi Matasa 5000 da Za'a Koya Masu Sana'o'i Domin Kada su Zama 'Yan Bangar Siyasa

Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai.

Ganin yadda 'yan siyasa ke yin anfani da matasa da basu da aikin yi a matsayin 'yan bangan siyasa, gwamnatin jihar Taraba ta debi matasa 5000 ta koya masu sana'o'i domin su samu madogara.

A karo na biyu gwamnatin jihar Taraba ta debi matasa dubu biyar a karkashin shirin tallafin raran man fetur da ake kira S-U-R-E-P.

Shirin na cikin yunkurin da gwamnatin keyi domin kawo karshen yin anfani da matasa a wajen tada rikici da jihar ke fama dashi cikin 'yan watannin nan.

Mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umaru yace gwamnatin zata cigaba da kirkiro da shirye-shirye da zasu taimaka hana zaman kashe wando. Shirin na farko Alhaji Garba Umaru yace sun anfana dashi sosai dalili kenan da suka ga ya kamata su yi na biyu domin yara, matasa da mata su samu abun yi kada 'yan siyasa su yi anfani dasu. Yau idan matashi ya samu sana'ar yi gwamnati ta bashi jari da kayan aikin da zai gudanar da sana'arsa shi matashin zai sake daukan wasu aiki ya koya masu sana'ar.

Akwai fannoni daban daban da za'a koyawa matasan. Abdulhadi Haruna Lau kwamishanan harkokin matasa da walwalar jama'a na jihar yace ma'aikatarsa ta dauki matasa dubu bakwai. Ma'aikatar dake kula da mata ta dauki matasa dubu daya da dari biyar. Akwai wasu dari da saba'in da biyar da zasu je su zama injiniyoyi. An tura wasu dari da saba'in Oron su koyi aikin man fetur. Kowane yaro dake samun horo a Oron gwamnati na kashe masa akalla nera miliyan biyu da dubu dari uku kowace shekara. Kawo yanzu jihar ta debi yara kusan dubu goma.

Sau tari akan yi anfani da matasa a matsayin 'yan bangan siyasa da kuma tada zaune tsaye.

Shugaban matasan jihar Kwamred Emmanuel Jet yace mukaddashin gwamnan ya kirkiro da shirin ne domin ya tabbatar matasa sun samu abun yi. Su kuma matasan jihar Taraba sun amince cewa irin mukaddashin gwamnan shi ne irin mutumin da su matasa suke bukata domin a cigaba da tafiya daidai. Yace yanzu matasansu sun fita harkar tashin hankali da sace-sace sun amince cewa yanzu suna da gwamnati da ta damu da rayuwarsu. Sun yi kuduri su goyi bayan gwamnatin yadda yakamata. Rokonsu shi ne Allah ya ba mukaddashin gwamnan karfi da hikimar yadda zai tafiyar da matasa yadda ya kamata.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Taraba ta Debi Matasa 5000 da Za'a Koya Masu Sana'o'i Domin Kada su Zama 'Yan Bangan Siyasa - 3'07"