Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Bijirewa Umarnin Turasu Daji


Manjo Janar Chris Olukolade
Manjo Janar Chris Olukolade

Wasu jami’an sojin Najeriya sun bayyana cewa, sun bijirewa umarnin turasu yakar kungiyar Boko Haram saboda basu da isassun makamai.

Wasu jami’an sojin Najeriya sun bayyana cewa, sun bijirewa umarnin turasu yakar kungiyar Boko Haram saboda basu da isassun makamai.

Sojojin sun ce, lamarin ya faru ne ranar asabar lokacinda aka umarci sojoji dake karkashin bataliya ta 21 su tafi Gwoza da Daiwa, garuruwa biyu a jihar Borno inda mayakan suke yawan kai hare hare.

Wani soja yace sojojin sun bijirewa umarnin lokacin da aka ce su yi gaba ba tare da motocin sulke na yaki biyu da aka ce za a yi amfani da su wajen kai farmakin ba.

Sojojin da suka nemi a saya sunansu sun bayyana haka ne a wata hira da manema labarai jiya Laraba a birnin Maiduguri.

A cikin sanarwar da ya bayar jiyar Laraba, kakakin rundunar ‘yan sojin Chris Olukolade yace bashi da wata masaniya game da lamarin, ya kuma musanta rahotannin cewa sun yi bore, bisa ga cewarsa, sojojin Najeriya suna da matukar kwarewa da kishin kasa saboda haka ba zasu aikata abinda ya zama babban laifi dake da hatsarin gaske ba.

Gwamnatin Najeriya tana ta kokarin yaki da kungiyar Boko Haram, da ake dorawa alhakin kashe dubban mutane a cikin shekaru biyar da suka shige.

Masu fashin baki sun ce da alamu mayakan sun fi jami’an tsaro manyan makamai. A farkon wannan watan matan sojojin bataliya ta 21 suka toshe hanyoyi domin hana tura mazansu Gwoza

XS
SM
MD
LG