'Yan gudun hijiran suna garuruwan Madagali da Mubi da Askira Uba inda tawagar ta ziyarcesu domin bada tallafi.
Wadanda ke gudun hijiran hare-haren 'yanbindiga suka rabasu da gidajensu a Gwoza da Damboa dake kudancin Borno. Sanata Ali Ndume dake wakiltar yankin kuma dan garin Gwoza yace mutanesu duk sun watse shi yasa a zamansa na shugaba mai wakiltarsu ya zo ya ga yadda suke ya kuma yi masu jaje. Yace mutum da aka rabashi da gidansa yana cikin mawuyacin hali.
Kodayake sun kawo gudunmawa ba abun da za'a dauka ana yayatawa a jarida ba ne.
Alhaji Muhammed Kanar babban jami'in hukumar bada agajin gaggawa na shiyar arewa maso gabashin Najeriya yace saboda yadda mutane suka kwararo daga Borno zuwa wajejen Madagali da Mubi da Askira Uba da sauran garuruka da dama dake yakin yasa suka yi hadin gwiwa da jihar Adamawa. Bayan haka sun tanadi kayan da suke kula da 'yan gudun hijiran dake Madagali da Askira Uba. Kayan da zasu kai Mubi ya taso yana hanya.
A wata sabuwa kuma kungiyoyin sa kai da na cigaban arewa ke mayar da martani ga kalamun tsohon shugaban Najeriya Janaral Ibrahim Babangida akan tabarbarewar tsaro. Alhaji Musa Jika na kungiyar fafitikar cigaban dan Adam yace maganar ba zata yi tasiri ba. Irinsu Babangida tamkar mushen gilaka ne. Sun mutu ne kawai amma suna ba yaro tsoro. Tunanensu sai yadda shugaban yanzu zai zarce da yin mulki. Lokacin da yakamata yayi magana bai yi ba.
Sakamakon hare-haren 'yan bindiga kusan mutane dubu hudu ne daga jihohin Borno da Yobe da ma Adamawa suke gudun hijira.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.