To amma duk da haka ta yi nasarar biyan albashin watannin Yuli da Agustan da suka gabata ta hanyar kudaden da ta ce ta tattara daga harajin cikin gida duk da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar a sanadiyyar juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Fira Ministan gwamnatin Rikon kwarya da ke bayani a taron manema labaran da ya kira ya fara da musanta kalaman da shugaba Macron na Faransa ya yi wa sojojin Nijer da yace sun kauracewa fagen daga don maida hankali akan maganar rike madafun iko. Ali Mahaman Lamine Zeine yace dakarun kasar sun kara jan damara a ci gaba da yaki da ta’addanci.
Ya kara da cewa gwamnatin rikon kwaryar ta tarar da billion ko kuma milliard 5200 na cfa na bashin da shudaddiyar gwamnatin Nijer ta ci daga cikinsu miliard 3200 daga kasashen waje abin da ke nufin bashi ya yi wa kasar katutu.
Sai dai duk da haka a cewarsa sun biya albashin ma’akata da jami’an tsaro na watannin Yuli da Agustan 2023 daga kudaden da suka samar a nan cikin gida daga lokacin da suka karbi madahun iko kawo karshen watan jiya.
A cewarsa sun dukufa wajen daukar matakan da za su taimaka daliban faramari da na sakandare da na jami’o'i komawa azuzuwansu a sabuwar shekarar karatun da ke shirin kamawa a watan gobe da dai sauarn bukatun al’umma.
Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce sun kaddamar da yunkurin ganin an cire wa Nijer dukkan takunkuman da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta kakaba wa kasar.
Haka kuma ya jaddada cewa a shirye kasar ta ke ta maida martani ga dukkan wani yunkurin amfani da karfain soja kamar yadda ECOWAS ta yi barazana a baya.
Batun hukunta masu laifuka, wato masu cin hanci da mahandama, na cikin abubuwan da fira minista ya tabo a ganawarsa ta farko da manema labarai.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5