NIAMEY, NIGER - Hakan na neman hanyoyin tunkarar kalubalen tsaro ne da ya shafi Nijar da makwaftanta, sai dai masu fafitika na ganin lamarin tamkar wata hanyar rufa rufa akan batun bai wa kasashen waje izinin girke dakaru a kasar ne.
La’akari da girman bukatar hada guiwa da kasashe aminai a yakin da ake gobzawa da kungiyoyin ta’addancin da suka addabi yankin Sahel ya sa gwamnatin ta Nijar bullo da wasu sabbin matakai da nufin inganta sashen dake bayani akan sha’anin tsaro a tsarin manufofin da Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya gabatar wa majalisar kafin ya kama aiki a watan afrilun 2021. Mafari kenan aka bukaci majalisar dokoki ta dubi wannan gyaran fuska.
To sai dai jami’an fafutika irinsu Maikol Zody na kungiyar Tournons la Page mai adawa da matakin girke dakarun kasashen waje ya ce wannan yunkuri ne na sakar wa kasashen Yammaci ragamar yi wa Nijar mamaya.
Honorable Kalla Moutari wanda tsohon Ministan tsaro ne na mai bada tabbaci a game da tasirin da wannan kwaskwarima za ta yi wajen neman bakin zaren matsalolin tsaron da ake fama da su. Dalili kenan da gwamnati ta yi kasadar gabatar da wannan kudiri a gaban majalissa don kawo karshen dukkan wani ce-ce-ku-ce.
A ranar Juma’ar dake tafe ne Majalisar za ta nazarci wannan bukata kafin a yi kuri’ar da a karshenta za a san makomar gwamnatin Ouhoumoudou Mahamadou ma’ana ko ta sami hadin kan ‘yan majalissa akan maganar karfafa huldar soja da kasashe aminai kafin a nan gaba a kai matakin neman izinin girke sojojin ketare.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5