Kimananin ‘yan canjin kudi su 100 jami’an tsaro na farin kaya suka cafke a kasuwar musayar kudaden waje ta Wafa ta Kano bisa tuhumar yin zagon kasa ga manufar gwamnati ta dakile hauhawar farashin Dala. Gabanin sumamen na Kano jami’an tsaron sun kai makamancinsa a Lagos da Abuja.
Daya daga cikin masu hada hada a kasuwar canjin ta Wafa, Adamu Isa Dan Juma, ya nuna rashin jin dadinsa ga sumamen da jami’an suka kai ba, kasancewar yanzu ana mulkin dimokaradiyya amma akai irin wannan sumamen kan mai uwa da wabi.
Shi kuma sakataren kungiyar masu canji ta Najeriya shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Yusuf Dan Gama, na ganin karancin takardun kudade na Dala shine babban abin da ya haddasa wannan matsala. Amma a zamansu da gwamnati tayi alkawarin samar musu da ita, su kuma zasuyi kokarin hana tashin farashin Dala.
Masanin tattalin arziki kuma shugaban sashen nazarin harkokin banki da kudi a kwalejin fasaha ta Kano, Mallam Lawan Habib, na ganin amfani da kudi ba zai sa gwamnati ta cimma burin na karya farashin Dala ba, kasancewar ba gurin gwamnati suke samun kudaden Dalar da suke bukata.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5