Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Kubutar da Mutane Goman da Aka Sace A Kuje, Abuja


Janar Abdulrahaman Dambazau ministan harkokin cikin gida
Janar Abdulrahaman Dambazau ministan harkokin cikin gida

Yayinda yake jawabi a Abuja ministan birnin Malam Muhammad Musa Bello ya fada cewa rundunar hadin gwuiwar jami'an tsaro ta kubutar da mutane goman da aka sace a karamar hukumar Kuje.

Kakakin ministan Abuja Abubakar Sani yace ministan ya sanarda duniya dangane da gagarumar nasarar da aka samu wajen kubutar da mutanen da aka sace aka kuma yi garkuwa dasu makon jiya.

Kakakin ministan yace basu biya kudin fansa ba saboda gagarumin shirin da jami'an tsaro suka yi. Injishi jami'an tsaron sun kewaye inda wadanda suka yi garkuwa da mutanen suke fakewa. Daga nan ne suka yiwa bata garin diran mikiya.

Shi ministan na Abuja yace a daidai lokacin da ake kokarin kubutar da mutanen wani jami'in tsaron farin kaya ya rasa ransa sakamakon rashin lafiya da ya samu.

Saidai yayinda ake farin cikin kubutar da mutanen sai gashi an sake sace wasu yara uku a karamar hukumar Kuje din.Umar Suleiman na cikin wadanda abun ya shafa domin an sace 'yarsa yar shekara biyu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG