A wani abu mai zaman yunkuri na farko da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a fanin Shari'a, aka kame wasu manyan alkalan kasar guda bakwai.
Kafin a bayar da belin alkali Sylveter Ngwuta, lauyoyin bangarorin biyu sun kai ruwa rana inda suka ringa tafka muhawara ‘daya bayan ‘daya ana zaiyana masa laifukansa 15, wanda suka hada da cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci na kudi sama da Naira Miliyan 500, baya ga zargin bada bayani na karya ga hukumar shige da fice a Najeriya.
Lauya mai kare jojin yayi bayanin nuna jin dadinsa ga yadda aka bayar da belin Sylvester Ngwuta a ranar farko na fara shari’ar inda yace “bada belinsa da akayi ya nuna cewa shari’a ta kankama kuma an kaucewa bata suna da jita jita kenan, yanzu shari’ar ce zata dauki hankalinmu zamuyi iyakacin kokarinmu na kare shi.”
Mai shari’a Sylvester Ngwuta yana daga cikin manyan alkalai bakwai wadanda jami’an tsaro na farin kaya suka kai sumame gidajensu a wani yunkuri na kawar da cin hanci da rashawa daga bangaren shari’a.
Domin karin bayani.