Muryar Amurka ta shiga daya daga cikin kasuwannin dake wani yankin birnin Abuja domin jin ra'ayin masu hada hada a kasuwar.
Saboda kusan duka masu saye da sayarwa a kasuwar sun tsorata babu wanda ya so yayi magana domin gudun kada allura ta tono garma.
Jibir Zakar wanda ya yadda ya tattauna da Muryar Amurka shahararre ne a kasuwar kuma an tambayeshi dalilin da ya sa yanzu dala tayi dan karen tsada. Yace babu abun da ya shafi canji da karya tattalin arzikin kasa. Yace idan gwamnatin Buhari na ganin kasuwar canji ce take karya tattalin arziki wane dan canji aka samu ya saci biliyoyin nera barkatai. Yace dan canji ba barawo ba ne. Dan kasuwa ne wanda yake kasuwanci kamar kowa.
To saidai masana tattalin arziki na ganin labarin daban saboda duk wani bangaren da ya shafi tattalin arziki dole ne a zuba ido a kansa domin samun mafita.
Yushau Aliyu masanin tattalin arziki yace kowace irin sana'a zata iya samun alaka da karya tattalin arziki kama daga noma zuwa kiwo har ma da aikin likita balantana kuma uwa uba kasuwar kudi. Kasuwar kudi nada mahimmanci domin nan ne ake daidaita farashin abun da talaka zai saya.
To saidai Malam Aliyu yace kasuwar canji tun daga babban bankin kasar ta samu matsala domin kudin babban bankin bai kamata ya shiga kasuwar canji ba. Ita kasuwar ta mutanen dake shigowa kasar ne su canza kudadensu amma sai ta rikide ta zama inda hatta masu neman kudin kasuwanci da biyawa 'ya'yansu kudin makaranta kasuwar suke zuwa. Sun bar bankuna.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.