Gwamnatin Najeriya ta soma rabawa 'yan gudun hijira kayan koyon sana'a

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari wanda ya cika alkawarin da yayi

Gabanin lokacin da ake kokarin kafa kwamitin da zai kula da mayarda 'yan gudun hijira zuwa garuruwansu a arewa maso gabas gwamnatin tarayyar Najerita ta soma raba masu kayan koyon sana'o'i daban daban

Tana raba kayan ne domin mutanen da zasu koma garuruwansu da aka kwato daga kungiyar Boko Haram su samu sana'ar yi saboda dogaro ga kai.

Yayinda yake raba kayan a madadin gwamnati sakataren gwamnatin ta tarayya Mr. Babacir Lawal yace manufar kokarin shi ne a tada komadar al'ummomin dake komawa domin su samu abun dogaro ga kai tare da murmurewa.

Hadimin shugaban kasa kan ayyuka da kuma tsare-tsare Onarebul Ibrahim Hassan shi ne ya kawilci sakataren gwamnatin tarayya a taron raba kayan. Yace gwamnatin Buhari ta damu da halin da al'ummomin ke ciki. Yace kullum ana cewa mutane su koma gida to idan suka koma me zasu yi. Dalili ke nan da gwamnati tace ya kamata a basu wani abu idan sun koma gidajensu zasu samu abun yi.

Kayan da aka raba sun hada da mashin mai buga blok, da keke napep, da injin markade, da keken dinki domin su koyi sana'a su samu abun da zasu yi.

Onarebul Hassan ya roki mutane kada su sayarda kayan da aka basu. An basu kayan ne domin su tallafawa kansu.

Fiye da mutane dubu daya aka rabawa kayan a Yola jihar Adamawa. Cikin kungiyoyin da aka rabawa kayan akwai ta musulunci da ta kirista.

Wadanda suka samu kayan sun yiwa Allah godiya da shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya yi alkawari ya kuma cika.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya ta soma rabawa 'yan gudun hijira kayan koyon sana'a - 3' 06"