WASHINGTON, D. C. - Ma’aikacin gwamnati mai mafi karancin albashi zai rika samun Naira 450,000 a shekara, kwatankwacin dalar Amurka 323.97 ko kuma 37,500 a duk wata, in ji Hukumar Samar da Albashi, da Kudaden Shiga da Hakkokin Ma’aikata Ta Kasa.
Karin albashin ya shafi dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka hada da na bangaren lafiya, ilimi da tsaro.
Gwamnati na tattaunawa daban-daban da kungiyoyin kwadago a kan sabon mafi karancin albashi na wata-wata na kasa, wanda tun a 2019 aka yi nazarinsa na karshe.
‘Yan Najeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da kashi 33.20%, wanda shi ne mafi tsanani a cikin shekaru 28 da suka gabata, bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur ta kuma daina daidaita darajar kudaden kasashen waje, lamarin da ya durkusar da darajar Naira.
Hukumar kula da wutar lantarki ta kasar kuma a wannan watan ta kara kudin wuta ga wasu masu amfani da wutar lantarki a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin yaye tattalin arzikin kasar daga tallafin da take bayarwa domin rage yawan dogaro ga kudaden gwamnati.
-Reuters