Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin NLC Da TUC Sun Bukaci Gwamnati Ta Biya Ma’aikata ₦615,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi


Kungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC
Kungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC

Kungiyar Kwadago ta kasa ta NLC tare da TUC ta ‘yan kasuwa, sun nemi gwamnati ta biya ₦615,000 ga ko wane ma’aikaci a matsayin mafi karancin albashi, sai dai wasu na ganin abu ne mai wuya idan an yi la'akari da zunzurutun bashin da ake bin Najeriya, wasu kuma suna ganin yaudara ce kawai.

Kungiyoyin sun tabbatar da cewa sun aike wa kwamitin da mataimakin Shugaban kasa ya nada domin duba yadda za a inganta albashin ma'aikata ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba.

Kwamred Nasir Kabir, shugaban tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa, ya ce mafi karancin albashin (₦615,000) shi ne abin da suka amince da shi, kuma a kansa za su tsaya, babu gudu babu ja da baya.

Nasir ya ce inda a ra'ayinsa ne, abin da ya kamata a biya ko wanne ma'aikaci ya zama akalla Naira miliyan daya duk wata.

Amma wata ma'aikaciya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, domin ko albashin dubu sha takwas da gwamnatin baya ta ce a biya ma'aikata har yanzu wasu jihohi ba su biya ba, balle kuma karin dubu talatin da gwamnatin baya ta yi. In an ce a daga zuwa dubu dari shida har da goma sha biyar, wa zai iya biya? Wannan yaudara ce kawai.

Yusha'u Aliyu kwararre a fannin tattalin arziki, ya ce ba lallai ba ne gwamnati ta amince da wannan bukata, domin za ta auna yawan ma'aikata da ta ke da su da kuma yawan kudin shiga da ta ke samu kafin ta amince. Saboda haka abu ne da zai zama sai an duba da idanun basira, domin a yanzu haka gwamnatin tana da basussuka da dama a kanta.

Ya zuwa yau dai ana bin gwamnatin Najeriya bashin akalla Naira Triliyan 87.9, kuma tuni har ofishin kididdiga ya fito da kiyasin cewa yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.20 a watan Maris din 2024 daga kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairun 2024.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Kungiyoyin NLC Da TUC Sun Bukaci Gwamnati Ta Biya Ma’aikata ₦615,000 Mafi Karancin Albashi.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG