Sanarwar da mashawarci na musamman a kan harkokin yada labarai ga Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, Nnemaka Okafor ya fitar, a yau Talata tace, an kitsa rahoton ne da nufin haddasa fitina da rudani a bangaren albarkatun man fetur din kasar.
Rahoton ya yi ikirarin cewa Lokpobiri ne ya baiwa kamfanin NNPCL umarnin.
Sai dai Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taba yiwa NNPCL katsalanda a kan farashin man fetur ba.
“Ma’aikatar albarkatun man fetur ba ta yi kuma ba za ta taba yin katsalandan shawarwarin cikin gida da NNPCL ya yanke ba, ciki har da batun farashi. Dukkanin wani hasashe da ya saba hakan ba wai kawai kuskure ba ne, ya ma bayyana rashin fahimta game da yanayin cefanar da bangaren albarkatun man fetur din Najeriya.
“Muna masu yin allawadai da wadannan zarge-zarge a matsayin marasa tushe kuma masu mummunar manufa sannan wani yunkuri ne na tunzara al’umma. Muna kalubalantar duk wanda yake da wata shaida; rubutacciya ko nadaddiyar murya ko faifan bidiyo game da wadannan zarge-zarge da ya fito ya bayyanasu.”
An ruwaito sanarwar na cewa, “ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya ta fito ta fayyace karerayin da ake yadawa a kafafen sada zumunta, dake ikirarin cewar Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya umarci kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya kara farashin man fetur sama da yadda aka amince dashi a hukumance.”