Gwamnatin Najeriya Ta Kare Matakin Hana Dalibai ‘Yan Kasa Da Shekaru 18 Rubuta Jarrabawar SSCE

  • VOA Hausa

Ministan Ilimin Najeriya, Tahir mamman

A watan Yulin da ya gabata, Ministan Ilmi Tahir Mamman yace daga shekarar 2025, ba za a sake kyale daliban da basu kai shekaru 18 da haihuwa ba su rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE).

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kare matakinta na haramtawa daliban da basu kai shekaru 18 da haihuwa ba rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE), inda ta zargi iyaye da yiwa karatun ‘ya’yansu zuku.

A watan Yulin da ya gabata, Ministan Ilmi Tahir Mamman yace daga shekarar 2025, ba za a sake kyale daliban da basu kai shekaru 18 da haihuwa ba su rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE).

Duk da cewa Ministan yace matakin bai ci karo da dokokin kasa ba, sai dai ya yamutsa hazo a fadin Najeriya, abinda ya janyo suka daga bangarori da dama.

Sai dai a yayin zaman bada ba’asi da ministoci suka yi a Abuja, Mamman ya kare wannan manufa wacce yace za ta haifar da da mai ido a nan gaba.

Ya kara da cewa, babu abin da ma’aikatar ilmi ta yi illa aiwatar da dokokin da dama akwaisu ba wai kirkirar sabbi ba kamar yadda wadansu ke hasashe.