Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Na Barazana Ga Miliyoyin Yara A Afrika.


Yara almajirai
Yara almajirai

Rahoton Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF bayyana ya ce daya a cikin yara 3 'yan kasa da shekara 5 a Najeriya suna fuskantar matsananciyar yunwa da rashin abinci mai gina jiki sakamakon rashin tsaro, sauyin yanayi, talauci da sauransu.

Wannan yasa masana suka karfafa bunkasa amfanin gona da hakan zai rage matsalar rashin abinci mai gina jiki a duniya musamman a yankin Afrika dake kudancin Sahel.

Yara 50 cikin 100 na fuskantar wannan matsalar ta rashin abinci mai gina jiki wanda hakan ka iya haddasa musu Tamowa wato ciwon yunwa dake da barazana ga rayuwar su.

A wani yunkuri na tallafa wa raya a kasashen Afirka game da irin wadannan matsaloli da suke fuskanta, shugaban gidauniyar Bill da Melinda, Bill Gates ya ziyarci Najeriya don inganta sabbin matakai a bangaren abinci mai gina jiki, lafiya da kuma harkar noma.

Da yake jawabi a taron matasan Afirka kan abinci mai gina jiki da aka gudanar a Abuja, Bill Gates ya ce za su maida hankali wajen yadda za a samar da abinci mai gina jiki duk da cewa ba abu ne mai sauki ba, amma za su hada hannu da banagaren lafiya, noma da kuma masana’antar abinci don samun nasara.

Ya ce shekara sama da 20 gidauniyar na bada tallafi a Afirka musamman Najeriya kuma ya yi farin ciki matuka game da ayyukan su, yana mai cewa sun yi nasarar rage mutuwar kananan yara sakamokon samun sabbin rigakafin cutuka dake da barazana ga rayuwar su.

Shin menene ma illar rashin abinci mai gina jiki musamman ga yara? Itace tambayar da na yiwa kwararren likitan yara Dr. Lawal Musa Tahir na Asibitin Nizamiye dake Abuja, wanda ya yi fashin baki a kan yadda yaran ke kasancewa idan sun kamu da wannan matsala.

Hajiya Maryam Mamman Nasir uwace kuma ta yi bayani wasu daga cikin dalilan da suka sa iyaye basa samun ciyar da yara da abinci mai gina jiki.

Malami a tsangayar koyar da ilimin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman dake Katsina Dr. Muntari Ado Matazu ya yi bayani kan irin nau’ukan abinci masu saukin samu da suka kunshi sinadarai masu gina jiki.

A Najeriya yanzu haka tashin farashin kayan masarufi musamman ma abinci a bisa alkaluman hukumar kididdiga MBS ya haura sama da kashi 33 cikin 100.

Ga rahoton Hauwa Umar cikin sauti:

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Na Barazana Ga Miliyoyin Yaran Afrika.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG