Gwamnatin Najeriya Ta Kara Kaimi Wurin Daukar Matakan Tsaro

Jami'an Tsaron Najeriya

Ganin yadda matsalar tsaro ke kara zama kalubale a Najeriya, kama daga karuwar hare haren mayakan Boko Haram a shiyar Arewa maso gabas, aika aikar ‘yan bindigar Zamfara a shiyyar Arewa maso yamma da aikace aikacen tsagerun Niger Delta, Gwamnatin Najeriya ta bayyana daukar sabbin matakan tsaron.

Ministan tsaron kasar, Bigediya Janaral Mansur Dan Ali ya gana da manyan hafsoshin sojojin kasar, inda kakakinsa Kanar Tukur Gusau ya shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa an umarci babban hafsan hafsoshin sojin kasa, Laftanar Janaral Tukur Buratai ya tare Maiduguri don sa ido kan yaki da ‘yan ta'adda na Boko Haram da akeyi a can.

An kuma umarci babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron kasar, Janaral Abayomi Gabriel Olonishakin da ya sake tsarin rundunonin Operation Delta safe dake aikin tsaro a shiyyar Niger Delta, da rundunar Operation Awatse a jihohin Legas da Ogun kana an umarci babban kwamandan Runduna ta takwas mai hedkwata a birnin sokoto da ya tare zuwa garin Gusau fadar jihar Zamfara don jagorantar yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Gwamnatin Najeriyar tace daga yanzu ta daina bada kwangilar sayo makamai a sojoji, maimakon hakan, daga yanzu za a yi cinikin makaman ne tsakanin gwamnati da gwamnati kai tsaye. Gwamnatin tana bayanin cewa zata sayo karin makamai na zamani ga dakarun kasar, sannan shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a kara inganta sha'anin walwalar sojojin kasar musamman wadanda suke aikace aikacen samar da tsaro a sassan kasar daban daban.

Yanzu dai abin jira a gani shine irin tasirin da wannan mataki zai yi wurin inganta sha'anin tsaron kasar da a halin yanzu ke kara tabarbarewa a daidai lokacin da kasar ke shirin tunkarar babban zabe badi idan Allah ya kaimu.

Ga rahoton wakilinmu Hassan Maina Kaina a kan haka:

Your browser doesn’t support HTML5

NAJERIYA TA KARA KAIMI A MATAKAN TSARON